Ganduje Ya Nada Sabon Sarkin Masarautar Rabo A Jihar Kano

0
432

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN jihar Kano ta amince da nadin Hakimin karamar hukumar Kibiya, Kabiru Inuwa, a matsayin sabon Sarkin masarautar Rano.

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ne ya sanar da hakan da yammacin ranar Talata yayin wata ganawarsa da manema labarai a Kano.

Alhaji ya ce Inuwa na daya daga cikin sunayen mutane uku da ma su alhakin nada sarki a masarautar su ka aikowa gwamnatin jiha.

Sauran mutane biyu da aka aiko da sunayensu su ne; Muhammadu Umar; hakimin karamar hukumar Bunkure da Munir Abubakar; chiroman Rano.

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci sabon sarkin ya kasance mai jajircewa wajen tabbatar da adalci a tsakanin talakawansa.

A ranar Asabar, 02 ga watan Mayu, ne Allah ya yi wa tsohon sarkin Rano, Tafida Abubakar Ila (Autan bawo), rasuwa. Ya rasu ya na da shekaru 74 a duniya.

A ranar Juma’a, 01 ga watan Mayu, aka kwantar da tsohon sarki Ila a asibitin koyarwa na Malam Aminu (AKTH) da ke birnin Kano bayan ya kamu da wata rashin lafiya da ba a bayyanata ba.

Daga bisani an mayar da shi asibitin kwararru da ke Nasarawa a birnin Kano , inda ya mutu washegari, ranar Asabar.

Masarautr Rano na daya daga cikin sabbin masarautu hudu da gwamna Ganduje ya kirkira a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here