Ministan Lafiya Ya Bayyana Maganin Covid-19 Da Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Shi

0
297

Daga Usman Nasidi.

MINISTAN lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya ce Najeriya ta fara amfani da wani magani mai suna ‘remdesivir’ a kan ma su jinyar cutar covid-19.

Da yake gabatar da jawabi a gaban mambobin majalisar wakilai ranar Talata, Ehanire ya ce da maganin ake amfani a kan masu jinyar cutar covid-19 jihar Legas.

Sai dai, ministan bai bayyana irin tasirin maganin a kan cutar covid-19 ba.

“Da remdesivir muke amfani; mun fara gwada shi a kan masu cutar covid-19 a Legas ,” a cewarsa.

A cewar ministan, an fara amfani da maganin ne domin ganin tasirinsa a kan kwayar cutar covid-19.

Ministan ya ce an kirkiri maganin ne tun asali domin maganin cutar Ebola tare da bayyana cewa Najeriya ba ta da wani zabi da ya wuce ta rungumi amfani da maganin domin maganin cutar covid-19.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu babu wani maganin gargajiya da aka amince da amfani da shi a kan ma su dauke da kwayar cutar covid-19.

Rahotanni sun bayyana cewa ma su jinyar covid-19 sun warke bayan an gudanar da gwajin maganin a kansu.

Kamfanin da ke kera maganin, Gilead Sciences, ya ce an gano cewa maganin ya na da tasiri a kan cutar covid-19 bayan an fara gwajinsa a kan ma su dauke da kwayar cutar a watan Fabrairu.

Sai dai, kamfanin ya ce har yanzu ba a kammala nazari a kan tsawon lokacin da ya kamata a dauka ana amfani da maganin a kan mai dauke da cutar korona ba.

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kasar Amurka (FDA) ta amince da amfani da maganin a kan ma su dauke da kwayar cutar covid-19 da aka kwantar.

Ya zuwa yanzu hukumar lafiya ta duniya (WHO) ba ta amince da amfani da wani magani ko rigakafin cutar covid-19 ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here