Buhari Ya Yi Wa Sarkin Daura Addu’ar Samun Lafiya

0
635

Rahoton Z A Sada

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya yi addu’ar samun saukin rashin lafiyar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar yake fama da ita.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malama Garba Shehu ya aike wa manema labarai ranar Laraba ta ambato shugaban kasar yana cewa ya “samu labarin rashin lafiyar ba-zata ta sarkin cike da tashin hankali kuma yana yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa.”

Sarkin Daura

“Ina bin sahun masarautar Daura da dukkan al’ummar jihar Katsina wajen yi wa Sarki Alhaji Umar Farouk Umar addu’ar samun sauki cikin gaggawa,” in ji Shugaba Buhari.

A ranar Talata ne aka kwantar da Sarkin na Daura a asibitin gwamnati da ke Katsina sakamakon larurar da ba a bayyana ba.

Wata majiya a fadar, wadda ba ta son a ambaci sunanta, ta shaida wa BBC cewa an fitar da Sarkin ne daga fadarsa da misalin karfe dayan dare na Talata inda aka garzaya da shi zuwa birnin Katsina.

Majiyar ta kara da cewa an kai Sarkin na Daura bangaren kulawar gaggawa na asibitin gwamnatin jihar. To sai an ce Sarkin yana samun sauki.

Kimanin kwanaki uku kenan dai da killace fadar Sarkin Daura bisa fargabar barkewar cutar korona a cikinta.

Gwamna Aminu Masari na Katsina dai ya ce tuni aka dauki samfurin majinar mutum 89 daga fadar domin yin gwaji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here