Haihuwa A Jirgi Ta Kawo Tsaikon Dawo Da ‘Yan Najeriya

0
293

Rahoton Z A Sada

JIRGIN da ya kwaso ƴan Najeriya daga Dubai ya koma bayan wata mata ta haihu a cikin jirgin jim kadan da tashinsa zuwa Legas.

Sanarwar da hukumar da ke kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje ta fitar, ta ce matar ta haifi namiji a cikin jirgin Emirates da ke ɗauke da ƴan Najeriya, minti 30 bayan ya baro Dubai.

Wannan ne ya tilastawa jirgin koma wa zuwa Dubai saboda matar, a cewar sanarwar.

Ta kara da cewa, matar tana asibiti yanzu haka ana kula da lafiyarta da ta jaririnta waɗanda ke cikin koshin lafiya.

Sanarwar ta ce an sauya jirgin, kuma yana kan hanya zuwa Legas ɗauke da ƴan Najeriya 265.

A jiya Talata ne ma’aikatar ƙasashen waje ta Najeriya ta ce za ta fara kwashe ƴan kasar da suka maƙale a wasu ƙasashe sakamakon hana tafiye-tafiye saboda annobar korona.

Ta ce za a kwaso tawagar farko ta ‘yan Najeriya 265 ne daga Dubai a ranar Laraba, sannan kuma a kwaso mutum 300 daga Landan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here