Kaso 80 Na Ma Su Cutar Korona Ba Sa Bukatar A Kwantar Da Su A Asibiti – Shugaban PTF

0
380

Daga Usman Nasidi.

KWAMITIN shugaban kasa na kar-ta-kwana a kan annobar covid-19 (PTF) ya yi gargadi a kan ajiye masu dauke da kwayar cutar korona da suke da koshin lafiya a cibiyar killacewa.

Shugaban PTF, Dakta Sani Aliyu, ya shawarci gwamnatocin jihohi a kan kwantar da duk wani mai dauke da kwayar cutar korona, inda ya bayyana cewa zai fi dacewa a ajiye kaso 80 na masu dauke da cutar a wurare masu kyau kamar Otal.

Dakta Aliyu ya bayar da wannan shawara ne ranar Laraba yayin taron da kwamitin PTF ya saba gudanarwa da manema labarai a kowacce rana.

Kazalika, ya shawarci jihohi su fara shiri na musamman a cibiyoyinsu na killacewa tare da samar da gadajen kwanciya da yawansu kar ya gaza 300.

Ya bayyana cewa ma su dauke da kwayar cutar da ba su galabaita ko nuna wasu alamun tsananin rashin lafiya ba, ba sa bukatar dawainiya mai waya, kawai sa mu su ido za a yi da saka masu wasu ka’idoji.

A cewarsa, ajiye su a wurare kamar Otal zai bayar da damar samun isashen wuri a cibiyar killacewa da ya kamata a kwantar da wadanda kwayar cutar ke galabaitarwa, sannan zai saukaka wa gwamnati kashe kudi.

Dakta Nasir ya roki dukkan ‘yan kasa su dauki annobar korona da muhimanci tare da yin gargadin, “ya zama dole mu yi duk wani abu da zai dakile yaduwar cutar yayin da ake kan matakin dokar kulle .”

A ranar Talata ne wasu masu dauke da cutar korona da ke jinya a cibiyar killacewa ta Kwadon da ke karamar hukumar Yamaltu Deba ta jihar Gombe sun fito zanga-zanga.

An gano cewa majinyatan na zanga-zangar ne sakamakon halin-ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna musu. Sun rasa abinci da magunguna duk da kuwa da killacesu da aka yi.

Wani mazaunin yankin wanda ya samu zantawa da manema Labarai, ya ce, “tabbas sun baro cibiyar killacewar kuma a halin yanzu suna tarwatsa dukiyoyin jama’a a kan babban titin.

“Abin takaici ne yadda majinyatan suka fito zanga-zanga. Gaskiya gwamnati ba ta yi musu adalci ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here