Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Kungiyar ISWAP Su 48

0
319

Rahoton Z A Sada

RUNDUNAR sojojin Najeriya ta ce dakarunta da na rundunar hadin gwiwar kasashe ta MNJTF sun kashe ‘yan kungiyar ISWAP 48 a wani hari da suka kai ta sama kan sansanin kungiyar da ke Dumba ranar Talata.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet ranar Alhamis, hedikwatar sojojin da ke Abuja babban birnin Najeriya ta ce sauran dakarun da suka kai harin sun hada da rundunar sojojin sama da dakarun rundunar Operation Lafiya Dole.

Sai dai rundunar ba ta bayyana ko an kashe wasu daga cikin dakarunta ba ko kuma sun ji rauni yayin harin da aka kai a kusa da Tafkin Chadi.

Wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Twitter ya nuna yadda rundunar ta kai harin daga sama.

Kazalika ta ce ta kai harin ne bisa bayanan sirri da ta samu cewa ‘yan kungiyar sun taru da niyyar kai hare-hare a makwabtan garuruwa, inda nan take jiragenta suka kai kai musu hari kuma suka ɗaiɗaita su.

Har wa yau, rundunar ta ce ta bi sahun dakarun kungiyar da suka kai wa sojojinta hari a kusa da garin Diffa na Nijar sannan ta kashe da dama daga cikinsu a wani matsuguninsu da aka yi wa lakabi da Location Charlie.

A watan Maris da ya gabata masu tayar da kayar baya a Najeriya suka kai hari kan wasu jerin motocin sojoji, inda suka kashe fiye da soja 40.

Hedikwatar tsaron kasar ta ce ya faru ne a wani kwanton-bauna da ake zargin mayakan Boko Haram da yi lokacin da sojojin suke aikin sintiri a kusa da dajin Sambisa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

A watan Satumban 2019 ma kungiyar ISWAP – reshin kungiyar IS a yammacin Afirka – ta ce ta kashe sojojin Najeriya biyu bayan ta kama su a wani hari da ta kai kan barikinsu a yankin arewa maso gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here