An Nada Ali Hassan A Matsayin Shugaban Riko Na Bankin Manoma

0
359

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Alwan Ali Hassan a matsayin Shugaban riko na Bankin Manoma, BoA.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Direktan Sadarwa na Ma’aikatar Noma da Raya Karkara, Theodore Ogaziechi, ya fitar ranar Alhamis inda ta ce Shugaba Buhari ya amince da rushe kwamitin wucin gadi mai kula da bankin nan take.

Hassan, kwararran ma’aikacin banki da ya yi aiki na fiye da shekaru 20 zai karbi ragamar jagorancin bankin manoman.

A cewar sanarwar, sanarwar nadin na cikin wasikar da Ministan Noma, Mohammad Nanono ya samu daga shugaban kasa mai lamba PRES/95/MARD/14.

Sanarwar ta kuma kara da cewa Mr Hassan dan asalin jihar Kano ne kuma yana da digiri na biyu a Fanin Kasuwanci sannan ya yi aiki a matsayin mamba na kwamitin amintattu na Orient Bank, Bank PHB da Platinum Capital and Trust Limited.

Shi ne kuma shugaban Midrange Universal Biz Ltd kuma mamba na Chartered Institute of Bankers da Nigerian Institute of Quantity Surveyors da wasu kungiyoyin.

Ya kuma samu horo a wasu fitattun makarantu na duniya da suka hada da MD Business School Lausanne, kasar Switzerland da Intrados Business School, Washington DC, Amurka.

BoA ce babban bankin manoma a kasar nan da ke da alhakin bayar da bashi da tallafi ga manoma da wasu ababen da za su inganta harkokin noma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here