An Samu Bullar Annobar COVID-19 A Yankunan Karkara – Gwamna El-Rufa’i

0
285

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNAN jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya bayyana damuwarsa game da karuwar matsalolin cutar COVID1-19 a yankunan karkara a jahar.

Gwamnan ya danganta yaduwar cutar ga tafiye tafiyen da jama’a suke yi, duk da haramcin da gwamnati ta yi a kan hakan, wanda hakan barazana ne ga al’ummar jahar.

A ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu ne gwamnan ya bayyana haka, inda yace yawancin masu cutar a Kaduna suna da tarihin tafiye tafiye, kuma hakan ne kara yaduwar cutar a Kaduna.

A cewar gwamnan, yawancin masu cutar sun fito ne daga kananan hukumomin Giwa, Igabi, Kaduna ta Arewa , Kaduna ta kudu, Makarfi, Soba da Zaria.

Daga cikin sabbin mutane 7 da suka kamu da cutar a jahar, hudu matafiya ne da suka dawo daga wajen Kaduna, daya kuma babban mutumi ne dake samun ziyarar baki dayawa.

Sai kuma sauran mutane biyu wanda mazauna barikin Yansanda ne, kuma sun kamu ne sakamakon mu’amala da suka yi da wani jami’in Dansanda da ya kamu da cutar.

Don haka kwamitin yaki da cutar a Kaduna ta yi kira ga jama’a su dinga lura tare da ankara da duk wanda suka san daga tafiya ya dawo, saboda rashin haka na mayar da hannun agogo baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here