Mahaifin Tambuwal Ya Rasu Yana  Da Shekaru 96 A Duniya

0
307
Mai alafarma Sarkin Musulmin Najeriya

GWAMNA Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya yi rashin mahaifinsa wanda da ya shafe shekarru 96 a duniya, Shaikh Haruna Waziri Usman yaya ne ga mahaifin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

Muhammad Bello mashawarci ga Gwamna a kan harkokin yada labarai ya fitar da sanarwar rasuwar wadda aka rabawa manema labarai a jihar Sakkwato ya ce Allah shi ne mamallakin komai  da haka yake sanar da rasuwar mahaifinsa Shaikh Haruna Waziri Usman.

Ya ce Margayin ya rasu ne a gidansa da ke garin Tambuwal a ranar Alhamis yana da shekarru 96, a duniya.

Shehi shi ne jagoran darikar Tijjaniya a garin Tambuwal gaba daya, ya yi wa addinin Allah hidima sosai al’ummar garin Tambuwal da jihar Sakkwato musamman mabiya darikar Tijjaniya sun yi rashin gwarzo mai son taimaka wa addinin musulunci

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here