‘Yan Bindiga 200 Sun Kai Hari, Sun Yi Wa Kauyuka 6 A Katsina Mummunar Barna

1
386

Daga Usman Nasidi.

AKALLA sama da ‘yan bindiga 200 dauke da miyagun makamai da suka hada da bindigogi kirar AK 47 suka kai hari kauyuka 6 na karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina.

Kauyukna sun hada da Tsugunni, Yandaka, Salihawar Duba, Garin Goje, Watangadiya da Dutse maizane inda aka hara a lokaci daya.

A yayin da aka kai harin a daren Alhamis, an gano cewa ‘yan bindigar sun dinga harbi. Sun yi nasarar kashe wani Alaramma Kabiru Kano mai shekaru 57 a kauyen Garin Goje.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar.

SP Gambo Isah ya kara da cewa, mutum uku ne suka samu miyagun raunuka a kauyen Dutse Maizane.

Ya kara da cewa, shanaye da tumaki masu yawa wadanda basu kirguwa ne ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su.

‘Yan bindigar sun kai harinsu har kan jami’an sojin Najeriya na hadin gwiwa da ‘yan sanda, wanda hakan ya kawo musayar wuta.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here