Kungiyar Kwadagon Jihar Kaduna Ta Tallafa Wa Marasa Karfi

0
363
Mustapha Imrana Abdullahi
KUNGIYAR kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna karkashin jagorancin kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ta tallafa wa mabukata da ke cikin al’umma da kayan abinci domin rage radadin zaman gida da ake ciki a kokarin hana yaduwar cutar Covid – 19 da ake kira korona da take addabar duniya.
Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya bayyana wa manema labarai a harabar ofishinsu da ke Kaduna cewa sun duba irin halin da wadansu mutane daga cikinsu ke ciki da suka rasa aikinsu tun a shekarar 2016 sai kuma musakai da dai sauran marasa galihu a cikin al’umma.
Kwamared Ayuba ya ci gaba da bayanin cewa daga cikin irin dan abin da kungiyar keda shi ne suke kokarin taimakawa wadansu domin Sanya farin ciki a Fuskokinsu.
Daga cikin abin da aka raba sun hada da Shinkafa mai nauyin kilogiram 10, Gero mai nauyin kilogiram 10 sai Man girki da abin wanke hannu da ake kira sanitizer.
An dai kira jama’a ne da suka hada da kabilu daban-daban daga cikin musulmi da kirista tare da kungiyar musakai da aka ba su gurbin mutane 20.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here