Kwamishinan Gwamna Tambuwal Ya Rasu

0
418

Rahoton Z A Sada

GWAMNATIN jihar Sakkwato ta tabbatar da rasuwar kwamishinan filaye da gidaje Surajo Gatawa.

Ya rasu ne a jiya ranar Lahadi inda aka yi jana’izarsa bayan sallar Magariba a Sakkwato, kamar yadda mai taimaka wa Gwamnan jihar kan harakokin watsa labarai Muhammad Bello ya tabbatar wa BBC.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce ya rasu ne bayan gejeruwar rashin lafiya. Amma ba a bayyana dalilin rasuwarsa ba a sanarwar ko nau’in rashin lafiyar da marigayin ya yi ba.

Kwamishina Gatawa

Marigayi Surajo Gatawa, Allah Ya gafarta masa kurakuransa,Ya sa Aljanna makoma

Marigayin wanda Allah Ya karbi ransa yana da shekara 63 a duniya, ya taɓa wakiltar Isa da Sabon Birni a majalisar Tarayya tsakanin 1999-2007, sannan ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Sabon Birni bayan ya yi kansila.

Ya rasu ya bar mata uku da ‘ya’ya.

Kamar yadda aka sani ne,cikin kwanaki biyu jihar Sakkwato ta yi rashin manyan mutane, da suka hada da tsohon karamin ministan Lafiya da ƙanin mahaifin Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here