A Koma Ga Allah A Bar Tsafi Da Bin Bokaye – Sheikh Abdulhadi

0
406

Rahoton Z A Sada

ABUBUWAN da Akur’ani mai girma ya yi maganarsu a wadansu zamunan da suka shude baya can, duk kwatance ne da hannunka-mai sanda ake yi mana mu all’ummar Manzon Allahh SAW, domin tsafe-tsafe da sihiran da misalin mutanen Fir’auna suka yi da izgilancin shi kansa Fir’auna da ”Zil autaad” nasa duka babu irin abin da ba a aiwatarwa a halin yanzu Don haka mafita kadai ita ce, mu tuba ga Allah tuba ta hakika, taubatun nasuha, kain azabarSa ta auko mana..

Sheikh Abdulhadi Aliyu Daura ne yake wannan batu a yayin fassarar Alkur’ani mai girma da yake yi na tafsirin Ramadan na masallacin Danfodiyo, Kaduna, inda ya ce,”Wallahi mutum yana cikin hadari domin bai san yadda mutuwa za ta riske shi ba, ita tana zuwa ne bagtatan”.

Sai ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu fada a ji a nan kasar da cewa, su yi hattara su guje wa saba wa Allah da Bokayensu suke sanya su. Ya ce, ana ta tsunduma al’umma cikin bata musamman mata, wadanda suke da raunin imani da ‘yan siyasa masu kwadayin mulki.

Sai ya ce idan mutum ya yi gam-da-katar ya jaddada imaninsa, to, zai iya kubuta daga kamun Allah da cin jarabawarSa a nan duniya, sannan ya sami tsira da rabo na gidan Aljanna a gobe kiyama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here