Ana Siyasantar Da Batun Annobar COVID-19 Da Almajirai Inji Gwamna Ganduje

0
379

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN jihar Kano ta gargadi wasu gwamnonin jihohin Arewa game da hadarin siyasantar da sha’anin annobar cutar COVID-19 da kuma halin da almajirai suke ciki a yankin kasar.

Mai girma Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a wajen wata zantawa da ‘yan jarida game da inda aka kwana wajen yaki da COVID-19 a jihar Kano, ya zargi wasu abokan aikinsa da rashin gaskiya.

Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jefi takwarorinsa da cusa siyasa a wajen yunkurin maida almajirai zuwa asalin jihohinsu da wasu gwamnatoci su ke yi a daidai wannan lokaci na annoba.

Idan ba ku manta ba, daga cikin daruruwan almajiran da gwamnatin jihar Kano ta maida jihohin da su ka fito kwanan nan, an samu wasu da-dama da ke dauke da kwayar cutar COVID-19.

Da yake hira da ‘yan jarida a Kano a ranar Lahadi, Abdullahi Umar Ganduje ya ce: “ Abin da wadannan almajirai suke bukata shi ne kulawa ba a yi ta ya-ma-di-di da labarinsu ba.”

Gwamna Ganduje ya karfafa cewa jihar Kano ta samu adadi mai tsoka na wadanda suka shigo mata da cutar COVID-19, amma ta zabi ta killace su, ba tare da ta fito tana wani surutu ba.

Bayan wannan gargadi da Gwamnan na Kano ya yi wa makwabtansa, ya koka game da yadda mutanen jiharsa ke watsi da dokar da shugaban kasa ya sa, ya ce akwai laifin jami’an tsaro.

Bayan haka kuma gwamnatin Ganduje ta ja-kunnen malaman addinin musulunci da suke shirin gudanar da sallar Juma’a da cewa su hakura da yin hakan domin zaman lafiyan kansu.

Bayan wannan rahoto da jaridar The Guardian ta fitar, idan za ku tuna gwamna Nasir El-Rufai ya fito ya na cewa an samu cutar COVID-19 a jikin almajirai 65 da aka dawo da su daga Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here