Buhari Ya Nada Mohammad Shehu A Matsayin Sakataren RMAFC

0
307

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin Mohammed Bello Shehu, a matsayin sakataren hukumar kasafin kudaden haraji da gwamnatin tarayya ta samu.

Shehu, wanda nadinsa ya fara aiki a ranar 19 ga watan Maris, zai shafe zangon farko mai wa’adin shekaru biyar a hukumar RMAFC tare da zabin sabunta nadinsa a zango na biyu idan shugaban kasa ya ga dama.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Willie Bassey, darektan yada labarai a ofishin sakataren gwamnatin tarayya. Sanarwar ta fito ne da yammacin ranar Litinin.

A cewar sanarwar, shugaba Buhari ya sake amincewa da nadin Bitrus Danharbi Chinoko a matsayin babban darektan CMD (Centre for Management Development) Lagos.
Nadinsa zai fara aiki daga ranar 27 ga watan Afrilu.

Kafin nadinsa a matsayin babban darekta mai cikakken iko, Mista Chinoko ya kasance mukaddashin babban darektan CMD.

“Shugaba Buhari ya taya su murna tare da bukatar su yi amfani da kwarewarsu domin kawo sauye – sauye masu amfani da muhimmanci a hukumomin da za su jagoranta ,” a cewar sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here