El-Rufai Ya Sanar Da Mutuwar Wani Babban Mutum A Jihar Kaduna

0
375

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNAN jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da rasuwar majinyata biyu sakamakon annobar Coronavirus, kwanaki takwas bayan sanar da mutuwar farko da jihar ta fuskanta sakamakon cutar.

A halin yanzu jihar Kaduna ta rasa mutum uku sakamakon annobar Coronavirus.

Na farkon ma’aikacin gwamnati ne wanda ya yi ritaya kuma yana da wasu ciwuka kafin annobar. Ya boye tarihin tafiyar da yayi zuwa Kano ko da ya ziyarci wani asibiti mai zaman kansa kafin ya koma na gwamnati.

Gwamna El-Rufai ya sanar da mace-macen ne a shafinsa na twitter. Ya ce daya daga cikin mamatan babban ma’aikacin jihar ne daga karamar hukumar Makarfi. Dayar kuwa mace ce daga karamar hukumar Zariya ta jihar.

Duk da bai bayyana sunayen mamatan ba, a daren Alhamis Gwamnan ya tabbatar da karuwar mutum bakwai masu cutar kamar yadda NCDC ta sanar.

Daga cikinsu kuwa akwai wani babban mutum a jihar wanda ya karba baki masu tarin yawa.

Kamar yadda ya sanar a shafinsa na twitter, El-Rufai ya ce a halin yanzu jihar Kaduna na da mutum 87 da aka tabbatar da suna dauke da cutar.

Ya ce mutum biyun da NCDC ta sanar da kamuwarsu a jihar da daren Asabar, akwai namiji daga Igabi sai kuma mace daga karamar hukumar Chikun.

Kamar yadda NCDC ta sanar, mutum 98 ne suka kamu da muguwar cutar a jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here