Gwamnatin Sokoto Za Ta Biya Malaman Sa-Kai Da Ke Aikin Jinyar COVID-19

0
342

Daga Usman Nasidi

GWAMNA Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya ba da sanarwar ba da alawus na N15, 000 a kowace rana ga wadanda suka zabi su yi aikin jinyar masu dauke da cutar COVID-19.

Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi alkawarin biyan wannan kudi ga malaman lafiyan da za su yi aiki a dakunan da ake killace wadanda su ka kamu da Coronavirus a jihar Sokoto.

Kwamishinan lafiya wanda kuma shi ne shugaban kwamitin da ke yaki da annobar COVID-19 a Sokoto, Ali Inname ya ce malaman lafiya fiye da 10, 000 suka bukaci su yi wannan aiki.

Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da mutane 1,000 na farko da aka zaba domin su yi aikin. Mai girma gwamna Aminu Tambuwal ya ce wasu za su yi aiki daga wajen dakunan jinyar.

Za a biya N12500 ga kowane daga cikin ma’aikatan jinyan da su ke aiki daga wajen dakunan killace marasa lafiyan. Sauran malaman asibiti za su samu karin 50% a alawus dinsu.

Ma’aikatan lafiyan da aka tura yankunan da ke kan iyaka a jihar za su samu karin 25% a na su alawus din a kowace rana. Likitoci da ungonzoma da leburori ne za su amfana da karin.

Da yake jawabi, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi alkawari cewa gwamnatinsa za ta samar da isassun kayan kayan aiki da na kare lafiya da malaman asibiti za su rika aiki da su.

Aminu Waziri Tambuwal ya ce za a rikidar da wasu otel da ke hannun gwamnatin jihar Sokoto su zama wurin killace masu cutar COVID-19.

Gwamnatin ta ce daga cikin wadanda aka fara dauka aikin akwai ungunzoma 106, malaman dakin bincike 30, masu ba da kayan magani 15, likitoci 44 da wasu ma’aikatan na daban

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here