Korona Bairos: Buhari Ya Amince A Karɓo Maganin Cutar Na Gargajiya

0
750

Rahoton Z A Sada

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin karɓo kason Najeriya na ganyen shayin Madagascar da shugaban kasar ya ce yana maganin cutar korona.

Sakataren gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, shugaban kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da korona ne ya bayyana haka a jiya Litinin yayin da yake yi wa manema labarai bayani, kamar yadda aka saba kan cutar korona a Najeriya da kuma matakan da gwamnati ke ɗauka.

Ya ce shugaba Buhari duk da ya amince a karbo maganin na Madagascar, kodayake ya kara da cewa dole sai ya bi tsari na tabbatar da ingancin magunguna.

Madagascar tuni ta aika wa kasashe da dama na Afirka da maganin kyauta, kuma ta tura zuwa Guinea Bissau.

Najeriya ta ce ya kamata ta karɓo nata kason daga Guinea Bissau.

Ya zuwa daren Lahadi, mutum 4399 aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Najeriya, mutum 778 suka warke yayin da mutum 143 suka mutu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here