Jihar Zamfara Ta Rasa Manyan Sakatarori Biyu

0
373

Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNATIN jihar Zamfara ta rasa wadansu mutane biyu masu matsayin manyan sakatarori sakamakon dan takaitaccen ciwo.

Manyan sakatarorin sun hada da Alhaji Yawale Dango, wanda ke aiki a ofishin shugaban ma’aikatan jihar sai Alhaji Ahmed Sale, da ke aiki a ma’aikatar gidaje da bunkasa yankunan karkara.

Sale dai ya mutu ne ranar Talata shi kuma Dango ya mutu ranar Laraba.

Tuni dai aka yi jana’izar su kamar yadda addinin Musulunci ya shimfida.

Da yake aikewa da sakon gaisawar ta’aziyya Gwamnan Jihar Zamfara ta hannun mai taimaka masa na musamman a kan harkokin kafafen yada labarai Alhaji Zailani Baffa, ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa mamatan ya kuma ba iyalansu hakurin jure rashin.

Matawalle ya kuma bayyana mamatan a matsayin mutane da ke aiki tukuru da suka sadaukar da kawunansu wajen yi wa jihar Zamfara aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here