Tazargade Ce Maganin Korona Da Aka Kawo Daga Madagaska – Inji Garba Shehu

0
396
Mustapha Imrana Abdullahi
AN bayyana Tazargade a matsayin maganin da kasar Madagaska ta ba Nijeriya domin a gwada a matsayin maganin cutar Korona.
Mai magana da yawun shugaban kasa a kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa kafar yada labarai ta BBC Hausa bayani a game da maganin da ake yayatawa kasar Madagaska ta ba Nijeriya.
A yanzu muna nan muna kokarin yin gwaji a kan inganci da nagartar maganin inji Garba Shehu.
“Tazargade ce fa”, inji Malam Garba Shehu.
Ya ci gaba da cewa a halin yanzu ana kokarin kammala duba irin yadda maganin da aka samar a Nijeriya yake wanda a yanzu ya wuce mataki na biyu a wajen gwajin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here