Bisa Kuskure Jami’anmu Suka Kashe Wani Dan Makaranta – Rundunar Sojin Najeriya

0
248

Daga Usman Nasidi

RUNDUNAR sojin Najeriya a karkashin atisayen OPSH a jihar Filato ta tabbatar da mutuwar wani matashi, Rinji Bala, mai shekaru 20, wanda yake aji uku a jami’ar Jos.

A ranar Talata ne dakarun rundunar OPSH suka harbi Bala, wanda aka fi sani da ‘Bobo’, a ofishinsu da ke kan titin zuwa Zariya a garin Jos, babban birnin jihar Filato.

Da yake tabatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar OPSH, Ibrahim Shittu, ya ce ba su ji dadin abin da ya faru ba.

A cewar Shittu mai mukamin Manjo a rundunar soji, jami’an rundunar OPSH sun samu kiran kar ta kwana a kan al’amuran wasu batagari, har ma suka kama matasa bakwai da ake zargi suna daga cikinsu.

Ya bayyana cewa daga baya sun sallami Bala da wasu sauran matasa hudu bayan sun gano cewa ba su da laifi, amma a hanyarsu ta fita daga ofishin, sai wani soja ya yi kuskuren tunanin cewa guduwa za su yi, lamarin da ya sa ya bude musu wuta.

“Da misalin karfe 10:00 na yamacin jiya (Talata), mun samu labarin cewa wasu ‘yan kungiyar asiri da ‘yan fashi da makami suna ofireshon a yankin Hwolshe.

“Rahoton da muka samu ya nuna cewa batagari suna amfani da dokar kulle wajen tafka ayyukan ta’addanci.

“Nan da nan jami’anmu suka dira yankin tare da kama wasu matasa bakwai da ake zargin da hannunsu a aikata laifin, kuma nan take aka taho da su ofis domin gudanar da bincike.

“Mun sallami biyar daga cikin matasan bayan bincikenmu ya gano cewa ba su da laifi, kuma nan take muka umarce su su bar ofishin.

“Amma, abin takaci, yayin da suke kokarin fita daga ofishin, sai wani jami’inmu ya yi tsammanin guduwa suke kokarin yi, lamarin da ya sa ya bude musu wuta har ta kai ga asarar ran Rinji Bala,” a cewarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here