Gwamnatin Jihar Naija Ta Kara Makonni Biyu Na Dokar Hana Zirga-zirga

0
314

Daga Usman Nasidi.

GWAMNAN jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya nuna damuwarsa da yadda mazauna jiharsa ke take dokar nesa-nesa da juna don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Bello ya sanar da hakan ne yayin jawabi ga manema labarai jim kadan bayan taron mako-mako da yake yi da mambobin kwamitin yaki da cutar korona na jihar.

“Abin takaici ne yadda muka rufe iyakokinmu tsakaninmu da wasu jihohin amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Masu babura suna yawan kaiwa da kawowa wanda hakan ke nuna karan-tsaye ga dokar gwamnatin.”

Gwamnan ya sanar da dokar hana aikin babura a jihar na makonni biyu yayin da duk sauran dokokin za su ci gaba da aiki na tsawon makonni biyun.

Yayin jaddada kokarin gwamnatin na ba da kariya ga ma’aikatan lafiya da kuma ‘yan kwamitin yaki da cutar na jihar, Bello ya tabbatar da cewa gwamnati za ta dauka mataki mai tsauri a kan harkar ma’aikatan lafiyanta.

Gwamnan ya yi kira ga jama’a da su kiyaye tsaftar kansu, zama nesa-nesa da juna, saka takunkumin fuska idan za a shiga jama’a da kuma gaggauta neman shawarar masana kiwon lafiya yayin da wata alamar cutar ta bayyana.

“Ina kira ga jama’a da suka san sun yi tafiya zuwa jihohin da cutar korona ta isa da su tabbatar da sun killace kansu da kuma kai rahoto ga cibiyar lafiya mafi kusa.”

Gwamnan ya bayyana cewa jihar na kokarin ganin ta samar da dakin gwaji a babban asibitin jihar da ke Minna don kara yawan samfur din da za a dinga gwadawa a kowacce rana.

Gwamnatin jihar Neja ta ba da umurnin rufe jihar a kan yunkurinta na yi wa manyan biranen jihar shida feshi.

Ya ce gwamnatin jihar ta horar da ma’aikatan lafiya 457 tare da daukar ma’aikata 20 na wucin-gadi don taimakawa a dakin gwaji.

Ya yi bayanin cewa gwamnatin ta kai magunguna da kayan kariya ga cibiyoyin killacewa na jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here