Masu Hali Ku Rika Bai Wa Talakawa Tallafi Maimakon Bai Wa Gwamnati-Garkuwan Hausa Fulanin Pengana

0
324
Alhaji Ya'u Bala Jingir.

Isah Ahmed Daga Jos

WANI mai taimaka wa al’umma kuma Garkuwan al’ummar Hausa Fulani na yankin  Pengana, da ke Karamar Hukumar  Bassa a Jihar Filato, Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi kira ga masu hali da kamfanoni na  kasar nan, su rika mika wa talakawa tallafin da suke bayarwa  kan halin da aka shiga na annobar korona, maimakon  bai wa gwamnati. Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Alhaji Ya’a Jingir ya ce shawarata ga masu hali da kamfanoni shi ne  su daina daukar kudin tallafin da suke bayarwa, don a tallafa wa talakawa  suna bai wa gwamnati, domin idan suka yi haka, tallafin ba ya isa wajen talakawa.

Ya ce duk wani mai hali ko wani kamfani ya san garin da yake, ya san unguwar da yake  kuma ya san mabukata. Don haka mai hali ko kamfani ya kafa kwamiti, ya bayar da wannan tallafi a wajen da yake, maimakon ya bayar da shi ga gwamnati.

Ya ce babu shakka idan masu hali suka taimaka ta hanyar sayen kayan abinci, suna tallafa wa mutane da suke zaune da su za a sami saukin wannan halin matsin da ake ciki.

‘’Ya kamata gwamnati ta tallafa wa mutane domin bai kamata a ajiye mutane a gida ba, alhalin ba su da abin da za su ci ba. Al’ummar Najeriya kashi 75 bisa 100, sai sun fita su sami abin da za su ci. Ka ga a ce an ajiye mutum a gida, kuma gwamnati ba ta ba shi wani tallafi ba,  akwai matsala’’.

Ya yi kira ga al’ummar Najeriya, su rika bin shawarwarin da jami’an kiwon lafiya suke bayarwa, kan kare yaduwar wannan annoba, kuma su ci gaba da rokon Allah, ya kawo karshen wannan annoba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here