Kotun Tafi-da-gidanka Ta Ci Sheikh Yusuf Sambo Tarar Naira Dubu 10 

0
1186
Mustapha Imrana Abdullahi
SHAHARARREN Malamin addinin Musulunci Sheikh Muhammad Yusuf Sambo Rigachikun ya tabbatar wa manema labarai cewa wata kotun tafi-da-gidanka ta ci tararsa tare da dansa naira dubu 10 a Kaduna.
Sheikh Yusuf Sambo ya bayyana cewa ya samu gayyata ne daga gidan Rediyon Jihar Kaduna ( KSMC) domin amsa wadansu tambayoyi domin amfanin al’umma baki daya.
” Na fita daga cikin gidana tun misalin karfe bakwai da wani abu domin cika lokacin da aka ce na gidan Talbijin na KSMC karfe takwas za a gudanar da shirin, don haka na isa kafin karfe 8 na safe, bayan mun kammala shirin sai na cewa dana da na tafi da shi wato Suhaibu, cewa mu tafi yi wa wani aminina Alhaji Ado Fara, ta’aziyyar mahaifiyarsa, bayan mun gama sai na ce mu bi ta titin Jami’ar jihar Kaduna KASSU, muna isa daidai mararrabar wurin sai na ga wasu ‘yan sanda ina tsayawa sai kawai wani ya ce mini ku je can ana nemanku, da isar mu na ga wata Alkaliya zaune a wurin wato Majistare ana ce mata Sa’adatu, kuma ga masu karbar kudi Tasks force”.
” Nan take aka ce mani an sa dokar batun Takunkumi kuma wanda ba shi da shi sai ya biya naira dubu biyar, ina tare da dana ne shi ma aka ce masa naira dubu biyar, kudi suka kama dubu goma, ba a tambaye ni ba’asin komai ba sai dai kawai in ba da kudi nan take na ciro na biya na ce a ba ni rasidi nawa daban na dana daban”. Inji Malam.
Malamin ya kara da cewa shi a iya saninsa ba haka ake yin lamarin kafa kotun shari’a ba sai a kai wa majalisar dokoki ta jiha su tabbatar da doka kuma a gayyaci jama’a a yi taron sauraren jin ra’ayin jama’a duk a Kaduna ba a yi hakan ba, sai kotun kawai ana yi wa jama’a tara duk da ga halin da ake ciki to, ina ga wanda ba shi da kudin da zai biya yana ta kansa ya samu abin da zai ci a ina zai nemo irin wadannan kudade?
Sheikh Sambo Rigachikun ya ci gaba da cewa ko kowa bai san tasirin yin addu’a ba mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sani domin lokacin da yake waje yana neman lafiya sai da kowane bangare na mutanen kasar nan ya dage yi masa addu’a Musulmi da Kirista kuma Allah ya karbi addu’ar an samu lafiyar tare da nasara.
“Ai idan lokacin zabe ya zo Malamai ake nema haka nan idan akwai wata musiba a kasa duk malamai ake nema domin su yi addu’a Allah ya kawo sauki a kasa, kuma game da wannan ciwo na Korona an ce an tambayi Ahaluzzikiri, wato ma’abota sani to mene ne ya sa a bangaren addini ba a tambayi Malamai ba domin a samu warware matsalar cikin ruwan sanyi”.
Kuma ma’abota ilimi da malamai duk sun san matsayin Masallaci da kuma kasuwa, amma an rufe masallatai an bude wasu kasuwanni na daban, to me ya sa?
Masallatai fa dakin Allah ne wurin yin addu’o’i, kasuwa kuma addini ya tabbatar mana cewa matattara ta wadansu irin mutane yana nan a cikin karantarwar musulunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here