Wasu Jihohin Arewacin Najeriya Sun Buɗe Masallatai Da Coci-coci

0
822
Mai alafarma Sarkin Musulmin Najeriya

Rahoton Z A Sada

A jiya Juma’a ne wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya za su bude wuraren ibada da aka rufe na tsawon makonni saboda daƙile yaɗuwar cutar korona.

Jihohin Borno da Adamawa da Gombe da Jigawa sun sassauta dokar wadda ta haramta yin taruka ciki har da na addini kuma yanzu mazauna yankunan za su iya zuwa masallatan Juma’a da majami’u.

Kazalika an buɗe Babbar Kasuwar Dabbobi ta Adamawa bisa sharaɗin za a bi ka’idojin yin nesa-nesa da juna.

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bukaci ‘yan jihar da kada su manta da kungiyar Boko Haram yayin addu’o’insu a sallolin dare, yana mai cewa “yanzu suna fama ne da annoba biyu”; Boko Haram da cutar korona.

A nasa bangaren, Gwamna Badaru Abubakar na Jigawa ya ce: “Mun sharɗanta cewa duk waɗanda za su shiga masallaci sai sun wanke hannayensu sannan su saka takunkumi da kuma bayar da tazarar mita biyu [tsakanin sahun salla]. Yawanci ana yi wa masallatan feshi kafin sallar Juma’a.”

Jihohin sun ce zuwa yanzu al’amura sun fara daidaituwar da za ta sa a sassauta tare da buɗe wuraren ibadar, kuma abin da ya sa suka yi hakan kenan.

Kazalika wasu malaman addinin Musulunci sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta jihar Kaduna da su sake bude masallatan Juma’a domin su yi salloli kamar yadda aka saba a baya.

Wasu daga cikin limaman masallatan sun bayyana fatansu na ganin matakin ya taimaka wurin dakile cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here