A Filato Mutum10 Masu Dauke Da Cutar Korona Sun Warke 

0
329
Isah Ahmed Daga  Jos
GWAMNATIN Jihar Filato ta bayyana cewa an sallami mutum 10, da suke dauke da cutar Korona, bayan an yi masu gwajin cutar an tabbatar cewa sun warke.
Da yake yi wa ‘yan jarida qarin bayani a wani taron ‘yan jarida a garin Jos babban birnin jihar, kwamishinan lafiya na jihar Dokta Nimkong Lar wanda ke tare da sakataren gwamnatin jihar Farfesa Danladi Atu da Kwamishinan watsa labarai na jihar Mista Dan Manjang,  ya bayyana cewa yanzu mutum 11 ne, suke jinyar wannan cuta ta Korona a jihar.
Ya ce mutum daya aka samu da wannan cuta jiya a Filato, sabanin bayanin mutum 5 da hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayar. Domin daga baya hukumar ta sake gwada mutum 4, kuma ta tabbatar cewa basu dauke da wannan cuta.
‘’A cikin mutum 21 da masu dauke da cutar Kurona da muke da su a jihar nan. Mun sallami mutum 10, bayan da aka tabbatar  yanzu basu dauke da wannan cuta, a gwajin da muka yi masu.  Don haka yanzu mutum 11 ne suka rage, wadanda suke dauke da wannan cuta a jihar nan. Kuma har ya zuwa wannan lokaci, babu wanda ya mutu sakamakon wannan cuta a jihar nan’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here