Korona Bairos: Buhari Ya Karɓi Maganin Gargajiya Na Madagascar

0
925

Rahoton Z A Sada

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya karɓi maganin gargajiya na Madagascar da Shugaba Rajoelina ya ce yana maganin cutar korona.

Shugaban ya karɓi maganin ne daga hannun shugaban ƙasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo wanda ya kawo wa Buhari ziyara tare da gabatar da maganin na Madagascar da ta raba wa ƙasashen Afirka, kamar yadda Malam Garba Shehu mai taimaka wa shugaban kan yada labarai ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar.

Sanarwar ta ce shugaban ya karɓi samfurin maganin, amma Buhari ya ce ba za a fara amfani da shi ba har sai masana kimiyya sun tabbatar da ingancinsa.

Shugaba Buhari tare da shugaban shugaban ƙasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco EmbaloHakkin mallakar hotoBASHIR AHMED
Image captionShugaban Guinea Bissau ya kawo wa Buhari maganin Madagascar

A ranar Litinin 11 ga Mayu shugaba Buhari ya bayar da umarnin karɓo maganin na Madagascar wanda ƙasar ta aika wa Guinea-Bissau domin raba wa sauran kasashen Afirka.

Yanzu Najeriya ta bi sahun ƙasashen Equatorial Guinea da Nijar da Tanzania da suka karɓi maganin.

Sanarwar da Garba Shehu ya fitar ba ta bayyana adadin yawan maganin ba da Najeriya ta ƙarba daga shugaba Embalo na Guinea Bissau.

Gwamnatin Nijar ta ce ta karɓi kwalin maganin da yawansa zai warkar da mutum 900, wato 300 masu ɗauke da cutar korona, 600 kuma a matsayin riga-kafi.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargaɗi kan kaucewa amfani da maganin da ba a tabbatar da ingancinsa ba.

Hukumar ta ce ba ta tabbatar da ingancin tasirin maganin na Madagascar ba, kuma babu wani binciken masana game da shi.

Zuwa yanzu mutum 5,445 suka kamu da korona a Najeriya, yayin da cutar ta kashe mutum 171, kamar yadda hukumar dakile cutuka masu yaduwa a kasar ta bayyana.

Masana binciken ingancin magani dai sun ce yadda cutar korona ke ci gaba da yaɗuwa a Najeriya ya kamata a gaggauta gudanar da binciken tabbatar da ingancin maganin Madagascar.

Shugaba Rajoelina ya ce amfani da maganin gargajiyar ne ya warkar da masu ɗauke da cutar korona a kasarsa. Ya kuma ce sun warke ne cikin kwana 10.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here