Rikicin PDP Reshen Filato Ya Dada Yin Kamari

  0
  382
  Isah Ahmed Daga Jos
  RIKICIN bangaran  jam’iyyar PDP  reshen jihar Filato, na tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Nasiru Mantu,  da bangaren tsohon Gwamnan Jihar Jonah Jang, ya dada yin kamari.  Bayan da bangaren Sanata Mantu suka  da kaddamar da sababbin  shugabannin riko na jam’iyyar. Karkashin  Honarabul Nandom Penap a matsayin sabon shugaban riko na jihar,  a sakatariyar jam’iyyar da ke garin Jos.
  Bangaren  Sanata Nasiru Mantu sun bayyana cewa sun dauki wannan mataki na rusa shugabannin jam’iyyar tare da kaddamar da shugabannin riko na jam’iyyar ne, bisa umarnin kwamitin amintattatu, na kasa na jam’iyyar.
  Da yake zantawa da ‘yan jarida kan wannan al’amari, bayan kaddamar da shugabannin rikon, sabon sakataren riko na jam’iyya  Inginiya Godwin Bendir, ya bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne ganin cewa tsofaffin shugabannin jam’iyyar, da suka rushe wa’adin shugabancinsu ya kare. Tun a ranar  10 ga watan nan na mayu, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar, na shekara ta 2017,  sashi na 47 [1] ya bayyana.
  Ya ce ganin wa’adin tsofaffin shugabannin jam’iyyar ya kare, shi ne kwamitin amintattu na kasa  ya bayar da umarnin   a dakatar da dukkan ayyukan jam’iyyar. Kamar yadda gwamnati ta bayar da umarnin a dakatar da dukkan wasu ayyuka, sakamakon halin da ake ciki na annobar coronavirus.
  ‘’Kwamitin amintattu na kasa  ya kafa wadannan sababbin shugabannin rikon ne, don su kula da jam’iyyar har ya zuwa lokacin aka sami saukin annobar da ake ciki na coronavirus, daga nan su sanya ranar da za azo, a zabi sababbin shugabannin jam’iyyar’’.
  A lokacin da aka tuntuvi jami’in watsa labaran jam’iyyar ta PDP reshen jihar ta Filato, Mista John Akans kan wannan al’amari, ya bayyana cewa  wadannan mutane da suke ikirarin cewa su sababbin shugabannin riko na PDP a Filato, ba ainihin  ‘yan jam’iyyar PDP bane.
  Ya  ce ‘yan jam’iyyar APC ne kuma APC  ce take daukar nauyin gudanar da wannan aiki, da suke yi.
  ‘’A yanzu da nake magana suna can suna taro da jam’iyyar APC. Suna son su wargaza jam’iyyar  ne  kafin su barta. A wajen ainihin ‘yan jam’iyyarmu ta PDP, mun yi nisa wajen yin tarurruka daban daban, don ganin mun warware banbancen da ke tsakaninmu. Kuma  har yanzu mune shugabannin riko na wannan jam’iyya’’.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here