Buhari Ya Bai Wa Sojoji Umurnin Fito-na-fito Da ‘Yan Bindiga A Katsina

0
561

Rahoton Z A Sada

SHUGABAN kasa, Muhammadu Buhari ya bai wa sojojin kasar umurnin gudanar da wani shiri na musamman domin fatattakar barayi da masu garkuwa da mutane da suka addabi jihar Katsina.

Shugaban ya ba da izinin ne a yayin da jama’ar jihar da ma wasu jihohi na makwabtanta ke kokawa kan ci gaba da tabarbarewar matsalar tsaro, wadda aka yi imanin ta yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane da raba dubbai da muhallansu cikin watannin baya-bayan nan kadai, duk da kokarin da hukumomi ke cewa suna yi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa a halin yanzu dakaru na musamman na nan na aiki, sai dai a cewarsa ba za a fallasa irin abubuwan da suke yi ba.

Ya shaida cewa tuni dakarun da ke da alhakin tsare-tsare suka isa jihar domin tsara wuraren da sojojin za su fi mayar da hankali domin yin wannan aiki.

Jihar wadda ita ce mahaifar shugaban kasa na cikin jihohin Najeriya da barayi da kuma masu garkuwa da mutane suka addaba.

A ‘yan kwanakin nan an samu rahotanni da dama na hare-hare da ‘yan bindiga ke kai wa musamman a kauyukan Batsari da Faskari da Jibiya da Safana da wasu kauyuka da ke jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here