Najeriya Ta Kama Jirgin Birtaniya Da Ke ‘Jigilar Fasinja

0
337
Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNATIN Najeriya ta kama wani jirgi na kamfanin Flair Aviation na kasar Birtaniya bayan zargin jirgin da laifin jigilar ‘yan Najeriya zuwa kasashen ƙetare da kuma shiga da su ƙasar.
Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya tabbatar wa manema labarai  da kama jirgin a wata tattaunawa inda ya ce yanzu haka ana gudanar da bincike kuma jirgin zai biya tara mai matukar yawa.
Ministan ya tabbatar da cewa jirgin yana jigilar mutane cikin Najeriya har zuwa jihohi kamar Abuja da Legas da kuma Oyo duk da annobar korona da ake ciki.
Ya bayyana cewa an bai wa jirgin damar gudanar da ayyukan jin ƙai, amma ya ɓuge da jigilar fasinjoji.
Tun a watan Maris ne gwamnatin Najeriya ta rufe filayen jirgin sama na kasar bisa la’akari da yadda annobar coronavirus ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.
Sai dai ko kafin rufe filayen jirgin, gwamnatin ta sanar da cewa jirage masu aikin jin ƙai kamar kawo kayan gwaji da magunguna za a ba su damar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here