Al’umomin Dawakin Tofa Da Rimin Gado Da Kuma Tofa Sun Yaba Wa Injiniya Tijjani Jobe.

0
577
JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
AL’UMOMIN kananan hukumomin Dawakin Tofa da Rimin Gado da kuma Tofa sun yaba wa wakilin su na majalisar tarayya Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe saboda kokarin da yake yi wajen samar da ayyukan raya kasa da ya yi a mazabar sa wanda hakan ta sanya zamantakewa take kara inganta a wadannan kananan hukumomi guda uku.
Mafiya yawan mutanen da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana cewa wakilin nasu ya cancanci yabo da godiya bisa kokarin da yake yi wajen gudanar da aikace-aikace na ci gaban al’uma kuma ba tare da nuna bambancin ra’ayi ko na siyasa ba, wanda hakan ta sanya kowane bangare na kananan hukumomi uku suke cikin yanayi mai gamsarwa.
Haka kuma mutanen mazabar sun bayyana cewa tun lokacin da suka fara tura Injiniya Tijjani Jobe zuwa majalisar wakilai a matsayin wakilin mazabarsu, a shekara ta 2007 suke amfana da wakilcinsa tare da samun ayyuka wadanda suka hada da samar da ruwan sha da kula da lafiya da harkar ilimi da tallafa wa mata da matasa da kuma samar da ayyukan yi ga al’uma.
Bugu da kari, al’umar mazabar ta Dawakin Tofa da Rimin Gado da Tofa sun sanar da cewa nan gaba kadan za su fara bayyana ayyukan alherin da dan majalisa Tijjani Jobe ya gudanar a kowace karamar hukuma domin tabbatar wa da duniya cewa yana wakilci mai amfani kuma za su ci gaba da ba shi goyon baya domin kara rabauta daga kyawawan manufofinsa.
A karshe, sun yi amfani da wannan dama wajen isar da sakon godiya ga Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe saboda raba kayan tallafi da ya yi a kananan hukumomi Dawakin Tofa da Rimin Gado da Tofa wanda ya taimaka kwarai wajen rage radadin zaman gida kan cutar Coronavirus da kuma azumi da ake yi a halin yanzu, tare da fatar cewa sauran wakilai su ma za su yi koyi da Tijjani Jobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here