Annobar Korona: An Sami Mutum Na Farko Da Ya Rasu A Filato

0
357
Isah Ahmed Daga  Jos
GWAMNAN jihar Filato kuma shugaban kwamitin yaki da yaduwar cutar annobar Korona a jihar, Simon Lalong ya tabbatar da cewa an sami mutum na farko da ya rasu, sakamakon kamuwa da wannan cuta. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummar jihar, kan matakan da gwamnatin jihar ta dauka na kare yaduwar wannan annoba a yammacin jiya Lahadi.
Gwamnan ya yi bayanin cewa a shekaranjiya aka dauki jinin wannan mutum da ya rasu,  domin a je a yi gwajin wannan annoba, amma kafin sakamakon gwajin ya fito, ya rasu.
Gwamnan ya ce an sallami mutum 10 da suke dauke da wannan annoba a jihar, bayan da aka yi masu gwaji aka tabbatar sun warke. Don haka tuni aka sallame su, suka koma cikin iyalansu.
  ‘’An dada sassauta dokar kulle a jihar zuwa kwanaki hudu a mako, maimakon kwanaki uku. Don haka daga wannan makon za a sassauta dokar daga ranakun Alhamis da Juma’a da Asabar da Lahadi. Daga nan kuma dokar ta ci gaba da aiki a ranakun Litinin da Talata da Laraba.  Gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki ne, domin ta dada sassauta wa al’ummar jihar kan mawuyacin halin da aka shiga sakamakon daukar wadannan matakai’’.
Gwamnan ya yi bayanin  cewa babban kalubalen da ake fuskanta a jihar, shi ne yadda ake karya dokar rufe kan iyakokin jihar, ta yadda  mutane suke shigowa jihar, ta wasu hanyoyin dazuzzuka daga wasu jihohi.
Ya ce wannan babban hadari ne ga jihar, kan wannan cuta domin dukkan wadanda suke dauke da wannan cuta a jihar sun fito ne daga wasu jihohi.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta rufe kasuwar ‘yan tumatur ta Farar Gada da ke garin Jos dalilin karya dokokin kare yaduwar wannan cuta na jama’a su nesanta juna da rashin tsafta. Ya ce idan aka rufe kasuwar ba za a sake budeta ba har sai shugabannin kasuwar da shugabannin karamar hukumar Jos ta Arewa sun kawo gamsashen tsarin kiwon lafiyar da aka yi a wannan kasuwa.
Har’ila yau ya ce rufe kasuwannin cikin garin Jos da gwamnatin ta yi sakamakon guje wa yaduwar wannan annoba yana nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here