Gwamna Ganduje Ya Amince A Yi Sallar Juma’a Da Idi

0
269

Rahoton Z A Sada

GWAMNAN jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya aminci da shawarwarin da wasu malamai suka ba shi na bayar da izinin yin sallar Juma’a da kuma Idi.

Sanarwar da Salihu Tanko Yakasai, mai bai wa Gwamnan shawara kan kafafen watsa labarai ya fitar ta ce gwamnan ya bayar da umurjin bayan ya tattauna da wakilan Malamai su 30 da kuma wasu jami’an gwamnatinsa ranar Litinin.

Sai dai ya ce ba za a bari mutane su yi shagulgula ba lokacin sallar Id, yana mai cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da dokar kulle.

“An umurci Malaman masallatan Juma’ah da su tabbatar duk wanda zai shiga masallaci sai ya saka safar fuska wato face mask da kuma wanke hannu da saka sanitizers, sannan a tabbatar an raba sahu kuma an rage huduba tare da rage cinkoso”.

Gwamnatin jihar ta bi sahun wasu jihohi ne wajen bari a gudanar da sallolin na Juma’a da na Idi.

Ganduje

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here