Za Mu Yi Adalci A Zaben Fidda Gwani Na APC Na Sanatan Filato Ta Kudu-Ustaz Barikin Ladi

  1
  977
  Ustaz Alhaji Ibrahim Barikin Ladi Sarkin Malamai

   Isah Ahmed Daga Jos

  USTAZ Alhaji Ibrahim Barikin Ladi Sarkin Malamai, shi ne  sakataren kudi na jam’iyyar APC reshen Jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya yi masu kama-karya a zaben fidda gwani na tsayar da dan takarar jam’iyyar APC, a zaben cike gurbi na kujerar Sanata, da za a gudanar mazabar Filato ta kudu.

  Har ila yau ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne maganganun da mutane suke yi, cewa akwai sabani tsakanin Gwamnan Filato Simon Lalong da Ministar harkokin mata Misis Pauline Tallen. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK: A matsayinka na jigo a jam’iyyar APC mene ne za ka ce kan zargin da ake yi wa gwamnatinku ta Filato na kasa tallafa wa al’ummar jihar a wannan lokaci, na cutar annobar Korona?

  Ustaz Barikin Ladi: Wannan magana ba gaskiya ba ce, domin ni din nan ina mai tabbatar maka shaida ne, haka  sauran  al’umma ma shaida ne, cewa gwamnatin Filato ta tallafa wa al’ummar jihar nan a wannan lokaci na annobar Korona. Sai dai mu ce idan danbu ya yi yawa ba ya jin mai. Amma daidai gwargwado, gwamnatin Filato ta tallafa wa al’ummar jihar nan, tun daga matakan kananan hukumomi zuwa mazabu, har ya zuwa akwatunan zabe. An bi an zabi mutane da suke da bukata, an tallafa masu da kayan abinci.

  GTK: Ana zargin Gwamna Lalong da niyar yin kama-karya, ta hanyar tsayar da wanda yake so, a jam’iyyarku a zaben Sanata na cike gurbi da za a gudanar a yankin Filato ta kudu, me za ka ce kan wannan zargi?

  Ustaz Barikin Ladi: Mu dama taken jam’iyyarmu shi ne adalci. Don haka a matsayinmu na iyayen wannan jam’iyya ta APC, ba za mu bari a yi mana kama-karya ba. Domin duk wanda yake cikin wannan jam’iyya, mu iyayensa ne. Sai da muka kafa wannan jam’iyya ta yi kyau ta zama abar sha’awa, sannan kowa ya zo ya nemi takara muka ba shi.

  Gwamna Lalong  ba shi da mukamin komai a cikin wannan jam’iyya. Ya shigo ne ya nemi takara muka ba shi, jama’a suka fito suka zabe shi, a matsayin Gwamnan jihar nan karkashin wannan jam’iyya.

   Don haka mu da kanmu muka kafa wannan jam’iyya, saboda haka ba za mu yarda wani ya zo ya yi mana kama karya ba. Domin mu ne shugabanni a wannan jam’iyya, don haka dole ne kowa ya yi mana da’a da biyayya a wannan jam’iyya.

  Saboda haka idan ka ji an yi kama-karya, a wannan zaben fidda gwani da za a gudanar, ba Gwamna ne zai yi  ba, sai dai idan mu ne za mu yi. Kuma mu ba za mu yi haka ba, domin taken jam’iyyarmu shi ne adalci. Don haka Gwamna bai isa ya yi mana kama-karya ba. Idan yau ya ce zai yi mana, za mu taka masa burki. Ba za mu yarda ba, kuma ba za mu bai wa wani kofa ya yi mana haka ba.

  Idan Gwamna ya fito ya ce yana son wannan mukami, wani ma ya fito ya ce yana son wannan mukami, kofa a bude take za mu ba shi dama, domin za mu dubi cancanta ne. Don haka wannan magana ta kama-karya, ba gaskiya ba ce.

  GTK: To mene ne za ka ce kan abubuwan da suke faruwa tsakanin Gwamna Lalong da ministar harkokin mata Misis Pauline Tallen?

  Ustaz Barikin Ladi:  Duk wanda za ka ji ya ce yana bangaren Gwamna Lalong ne, ko yana bangaren Pauline Tallen ne yana fadin ra’ayinsa ne kawai, domin a jam’iyya kowa yana da ra’ayinsa.  Amma idan muka koma gida ai Pauline Tallen, uwa ce ga Gwamna Lalong, don haka duk yadda za ka yi ka raba su ba zai yiwu ba. Saboda haka duk masu cewa akwai sabani tsakanin wadannan mutane suna fada ne kawai. Amma gaskiyar magana babu wata matsala, tsakanin wadannan mutane biyu.

  GTK: To, mene ne za ka ce kan rikicin da ke faruwa, a jam’iyyar adawa ta PDP reshen   Filato?

  Ustaz Barikin Ladi: Ka san wannan jam’iyyar adawa ta PDP babu adalci a cikinta. Ita tana gadara da karfin mulki  da kama-karya ne kawai.  A yi kama karya a nuna karfi, a yi abin da ake so a yi. Don haka muke ba su shawarar su dawo jam’iyyar APC mai adalci, domin a yi masu adalci. Domin duk jam’iyyr da ta tsaya kan adalci za ta cimma nasara. Rashin gaskiya da adalci  ne ya sa jam’iyyar PDP ta  shiga cikin wannan rudani.

  GTK: Ganin irin koke-koken da jama’a suke yi, kan yadda kuke tafiyar da mulki, kana ganin za ku iya samun nasara, a zaben shekara ta 2023?

  Ustaz Barikin Ladi: Wato abin da yake faruwa, idan ka duba  duniya ce gabaki daya ta shiga cikin wani mawuyacin hali. Abin ya shafi kowa da kowa ne. Domin idan mutum ya dubi yadda yake sarrafa gidansa a da, yanzu idan  bai tashi tsaye ba, ba zai iya yi ba. Balle  mulki irin na jama’a.

  Mu dai muna kokari mu hado kan jama’a, don mu fuskanci wannan annoba da ta addabi duniya baki daya.

  Kuma abin da nake son a lura, shi ne duk adawar da ake yi kan abubuwan da suke faruwa musamman gwamnatinmu ta  Filato, ba jam’iyya aka zaba ba, an zabi cancanta ne. Don haka a nan gaba ma za mu dubi, mutumin kirki mai gaskiya da adalci ne mu zaba, ba tare da duba jam’iyyar da ya fito ba. Don haka ina ganin babu abin da zai hana mu samun nasara a zaben shekara ta 2023, saboda gwamnatinmu ta Filato ta taka rawar gani fiye da gwamnatin da ta gabata.

  Domin a da muna cikin yake-yake ne a jihar nan, amma yanzu muna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali da lumana.

  Babu shakka a yadda Filato take yanzu, mun taka rawar da gwamnatocin baya da suka gabata ba su taka ba. Saboda haka da yarda Allah, babu wata damuwa a wannan gwamnati, domin idan za a yi zabe sau goma a jihar nan mu ne za mu yi nasara.

  GTK: Wanne sako ne kake da shi zuwa ga al’ummar Filato?

  Ustaz  Barikin Ladi: Sakona ga al’ummar Filato shi ne mu rungumi juna mu zauna lafiya, mu gaya wa junanmu gaskiya. Mu taru mu zabi mutumin kirki a zabe mai zuwa na shekara ta 2023.

  1 COMMENT

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here