A Fara Neman Wata Ranar Juma’a Amma Da Wuya A Gani – Sarkin Musulmi

0
337
Mai alafarma Sarkin Musulmin Najeriya

Daga Usman Nasidi

SHUGABAN Majalisar koli ta shari’ar Musulunci a Najeriya NSCIA kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni ya yi kira yan Musulmai su nemi watan Shawwal ranan Juma’a.

Mai Alfarman ya bayyana hakan ne a jawabin da Majalisar NSCIA ta saki ranar Litinin inda yayi wasu bayanai game rashin yiwuwan ganin watan amma dai kawai a nema.

Ya bayyana cewa Musulman Najeriya su saurari sanarwarsa domin sanin ranan karewar watar Ramadanan bana.

Jawabin yace: “Bisa ga shawaran kwamitin neman wata, ranar Juma’a, 22 ga Mayu, 2020 wanda yayi daidai da 29 ga Ramadana 1441AH ne ranar fara neman watan Shawwal 1441AH.”

“Amma a ranar, watan zai fito yan mintuna kadan kafin rana ya fadi wanda hakan ke nufin ganin watan ba zai yiwu ba.”

“Amma dai, shugaba, bisa ga sunnar Manzon Allah (SAW) ya yi kira ga al’ummar Musulmi su nemi watar Shawwal 1441AH bayan faduwar ranar Juma’ar.”

“Ana kira ga dukkan Musulman Najeriya su saurari sanarwar mai alfarma, shugaban NSCIA, kan karewan watar Ramadana.”

Bayan haka, kwamitin neman watan tarayya ta raba wani faifan bidiyon wani matashi a Tuwita inda yake bayani kan rashin yiwuwar ganin wata ranar Juma’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here