An Bayyana Halin Cutar Korona Da Ake Ciki A Matsayin Jarabawa Daga Allah

0
426
Mustapha Imrana Abdullahi
SHUGABAR kungiyar wa’azi da yada addinin Musulunci IMWON ta kasa Malama Rabi’ah Ahmad Sufuwan, ta bayyana hakuri, Juriya da komawa ga Allah a matsayin abin da ya dace a yanayin da ake ciki na Covid – 19 da ake kira Korona bairos.
Ta bayyana hakan ne lokacin da ta ce ganawa da manema labarai a Kaduna
Malama Rabi’ah Sufuwan ta ci gaba da cewa abin da ake bukata a tsakanin al’umma Maza da Mata cikin yanayin Korona bairus da ake ciki shi ne hakuri, juriya da ganin girman Juna a tsakanin magidanta Maza da Mata.
Ya dace maza su sani cewa ba fa mata ne suka kawo wannan cutar ba da har wasu suke kasa yin hakuri da yanayin iyali har sai a rika kai wa yara duka sakamakon bacin rai, duk baki daya hakuri da juna ne kawai magani har Allah ya ba jama’a ikon cin jarabawar da ake ciki.
Malama Rabi’ah ta kuma yi kira ga daukacin mata musulmai da su yi koyi da irin halayen Matan Manzon Allah Annabi Muhammadu (SAW) domin yin hakan zai kara inganta yanayin zamantakewa a tsakanin maza da matansu.
“Hakika hakuri da juriya tare da ganin mutuncin Juna ana girmama kowane bangare tsakanin Maza da Mata ma’aurata zai taimaka wa rayuwar zaman aure da tafiyar zamantakewa baki daya, kuma zai taimakawa wajen cin jarabawar da Allah madaukakin Sarki ya dora wa duniya sakamakon Korona bairos”. Inji Rabi’ah Sufuwan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here