Gwamna El Rufai Da Ganduje Suna Zaman Doya da Manja

0
380

Rabo Haladu Daga Kaduna

ZA a iya cewa abin boye ne kawai ya fito fili cikin mako biyu da ya gabata tsakanin Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da takwaransa na Kaduna, Nasir El-Rufa’i, bayan Gwamnan Kanon ya mayar wa da na Kaduna martani.

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i dai ya ta nanata cewa mafi yawancin masu cutar korona a jiharsa almajiran da Gwamna Ganduje ya mayar da su ne daga Kano.

Wannan magana ba ta yi wa Ganduje dadi ba, inda ya mayar da martani a wata sanarwa cewa”Yadda muke mayar da almajirai jihohinsu, haka mu ma ake dawo mana da almajirai ‘yan asalin jihar Kano daga wasu jihohin.

El-rufai da Ganduje

Don ba ma yin surutu a kan batun, ba yana nufin dukkansu lafiyarsu kalau ake kawo mana ba, ko ba sa dauke da COVID-19.”

To sai dai masu fashin bakin siyasa na cewa sa-in-sa ta baya-bayan nan ta fito da wata jikakkiya da ke tsakanin Gwamnonin biyu.

Malam Kabiru Sufi wani masanin kimiyyar siyasa a Kano ya shaida wa BBC cewa alaka tsakanin gwamnonin biyu ta yi tsami ne bayan da Gwamna Ganduje ya yi biris da neman alfarma da mutane irinsu El-rufa’i suka yi a wurinsa don kada ya tube rawanin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

An dai ce Gwamna El-rufa’i da wasu gaggan jamiyyar APC sun ta faman ganin an samu sulhu tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi amma hakan ya ci tura.

Malam Kabiru Sufi ya ce “ina kyautata zaton wannan abu bai yi wa Nasir El-rufa’i dadi ba kuma daga nan ne alaka ta fara tsami tsakanin shugabannin biyu”.

Ya kara da cewa “kafin nan ai Ganduje da El-rufa’i suna shan inuwa daya kuma akwai bayanai masu karfi da ke nuna Bola Ahmed Tinubu da El-rufa’i sun taka gagarumar rawa wajen ganin Gwamna Ganduje ya ßAbubuwan da Elrufa’i ya yi domin huce takaici

Jim kadan bayan sanar da tsige Sarki Sanusi da gwamnatin jihar Kano ta yi, Gwamna Elrufa’i ya sanar da nada tsohon sarkin a matsayin uban jami’ar jihar Kaduna, KASU.

Har wa yau, El-rufa’i ya sake bai wa Muhammadu Sanusi II mukamin mataimakin shugaba a majalisar magabata ta hukumar bunkasa zuba jari ta jihar wadda ake kira KADIPA, kwana guda bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauke shi daga gadon sarautar Kano.

Bayan kimanin mako guda kuma Gwamna El-rufa’i ya kai wa Muhammadu Sanusi ziyara garin Awe na jihar Nasarawa, inda ya yi masa rakiya zuwa filin jirgin birnin Abuja kafin tashi ya nufi birnin Legas.

Malam Kabiru Sufi ya ce “watakila Nasiru Elrufai ya yi duk wadannan ne domin ya huce haushin kin sauraronsu

Malam Kabiru Sufi ya ce “lokuta da dama zaman doya tsakanin shugabannin al’umma kan yi tasiri a kan mutanen da ake jagoranta.

Don haka ni ina ganin wannan abu zai yi tasiri a kan abubuwa guda biyu – yaki da annobar korona da kuma yadda za a

To kyautata zaton zaman doya da manjan da ake kallon gwamnonin biyu suna yi bai zama lallai ya ta’azzara ba kasancewar halin mutanen biyu ya sha banban.

“Shi Abdullahi Umar Ganduje ba mutum ne mai son sa-in-sa ba amma yakan tara laifin da aka yi masa har zuwa lokacin da zai dauki fansa, inda shi kuma Gwamna Elrufa’i mutum ne mai hali irin na sha yanzu magani yanzu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here