Gwamnan El-Rufa’i Ya Yi Wa Malamai ‘Allah Ya Isa’

0
314

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNAN jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi wa malaman da suka zargesa da hana sallar Juma’a a jihar ‘Allah ya isa’.

Gwamnan ya ce ya bar malaman da Allah ne a jawabin da ya yi ga ‘yan jiharsa a yammacin ranar Talata.

A cewarsa, “Ko a makka ba za a yi sallar idi ba amma mu a nan malamai sun hau mumbari suna cewa mun hana sallah. Saboda haka Allah ya isa. Na yafe wa duk wanda ya zage ni amma ba zan yafe wa wanda ya yi min kazafi ba.”

Gwamnan ya tabbatar da cewa ba zai bar kowanne mutum shiga jihar Kaduna a ranar Sallah daga Kano ba. Kasancewar gwamnatin jihar Kano ta amince da gudanar da sallar Idi da Juma’a.

“Da kaina zan je hanyar shigowa Kaduna daga Kano na ga mutumin da zai shigo mana. Cuta ta riga tayi katutu a tsakanin mutane. Mu kuwa ba za mu bari su shigo mana da ita ba. Ba zai yuwu ba,” in ji El-Rufai.

Ba kamar wasu jihohi ba, El-Rufai ya ce kowa yayi sallar idi da Juma’a a gida don dakile yaduwar cutar korona da ke yi wa duniya barazana.

Har ila yau, gwamnan ya zargi jami’an tsaro da cin amana inda ya ce suna karbar na goro domin barin jama’a su shiga jihar Kaduna.

Gwamna Nasir ya ki sanar da lokacin da ake tsammanin bude jihar. Mataimakiyarsa ta ce har yanzu basu gamsu da yanayin da cutar take ba ballantana su bude jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here