Ni Da Kai Na Zan Fita Tsare Iyakokin Kaduna-Kano A Ranan Sallah — El-Rufa’i

0
379

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

GWAMNAN Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce shi da kansa zai fita domin tsare iyakokin Kaduna da jihar Kano a ranar Sallah domin tabbatar da cewa babu wani da ya shigo jiharsa daga Kano a yunkurinsa na dakile yaduwar cutar korona.

Ana sa ran za a gu danar da bikin sallar na wannan shekarar a ranar Asabar ko Lahadi ne idan azumin watan Ramadan ya zo karshe.

Tuni dai gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita inda ta ware wa mutane kwanaki biyu domin su fita su siya kayayyakin da suke bukatar a ranakun Laraba da Alhamis don tabbatar da kowa ya zauna a gida a karshen makon.

El Rufai ya yi wannan gargadin ne a yayin hira da aka yi da shi a wasu gidajen rediyo a ranar Talata inda ya ce; “Da kai na zan fita in rika zaga iyakokin Kaduna da Kano kuma ba zan bar wurin ba sai dare don in ga wanda zai shigo Kaduna. Ba zan bar wurin ba sai dare.”

Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda mutane ke shiga da fita jihar duk da umurnin shugaban kasa na hana zirga zirga tsakanin jihohi, inda ya ce galibin wadanda suke dauke da cutar a jihar sunyi tafiya.

Ya jingina laifi a kan wasu jamian tsaro marasa kishin kasa da ke karbar cin hanci a hannun matafiya su barsu su shigo jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

El Rufai ya ce, “Ba abinda ba mu yi ba amma jamian tsaro ba su bamu hadin kai. Mun samu labarin yadda wasu direbobin motocin haya da wasu ke biyansu kudi don su shigo Kaduna.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here