An Ki Karbar Wani Sabon Fursuna A Kan Fargabar Korona A Kaduna

0
323

Usman Nasidi, Daga Kaduna

HUKUMAR gyaran hali ta jihar Kaduna ta ki karbar wani sabon fursuna da Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ta kawo mata.

Shugaban gidan gyaran halin Sanusi Danmusa, a ranar Juma’a ya ce an ki karbar sabon fursunan ne saboda kare wadanda ke gidan gyaran halin daga kamuwa da COVID-19.

Ya ce gidan gyaran halin ta daina karbar sabbin wadanda aka yanke wa hukunci har ma da masu ziyara saboda bullar annobar ta coronavirus.

An yanke wa Sadiq Musa, mai sana’ar canjin kudi hukucin zaman shekaru bakwai a gidan gyaran hali ba tare da zabin biyan tara ba.

Da yake tsokaci a kan rashin karbar fursunan, shugaban hukumar EFCC na Kaduna, Yakubu Mailafia ya ce bai san inda hukumar gidan gyaran halin take so ya kai wanda aka yanke wa hukuncin ba.

Ya ce, “Hukumar EFCC tana da ka’ida game da tsare masu laifi kuma gidan gyaran hali shi ne wuri na karshe da ake kai wadanda aka yanke wa hukunci, ina za mu kai su?”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here