Buhari Da Gwamnoni Sun Kulla Yarjejeniya 5 A Kan Bude Masallatai

0
381

Daga Usman Nasidi.

A yayin da ake ci gaba da tsoron yaduwar annobar korona sakamakon dage dokar hana sallar jam’i, shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnoni sun yi taro a ranar Alhamis, 21 ga watan Mayu.

A nan ne kuwa suka kulla yarjejeniya biyar a kan yadda za a ci gaba da yakar annobar korona a kasar nan.

Gwamnoni shida na yankin arewa da suka hada da Gwamna Ganduje na jihar Kano sun dage dokar hana jam’i a jihar don a samu a yi sallar Idi.

Jama’a da yawa sun kalubalanci wannan matakin don ya saba wa shawarar kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar korona da kuma hukumar NCDC.

A ranar Juma’a, 23 ga watan Mayu, shugaba Buhari da kungiyar Gwamnoni sun yi taro inda suka amince da bude wuraren bauta tare da yin sallar jam’i amma kada a zarta mutum 50.

Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya tabbatar da cewa yin taron har da kungiyar Kiristocin Najeriya.

Fayemi ya samu zantawa da shugaban majalisar koli ta addinin Musulunci, Sultan Sa’ad Abubakar IIi a kan dage dokokin takaita zirga-zirga da kuma na hana zuwa wuraren bauta.

Gwamnonin sun aminta da cewa ba a sauya dokar hana taron jama’a ba, kuma babu Gwamnan da zai karya wannan dokar.

A wani gefe na daban, wani Gwamna daga yankin arewa maso yamma ya bayyana cewa yarjejeniyar da suka zartar da shugaban kasar ya shafi Kiristoci da Musulmai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here