Dalilin Da Ya Sa Muka Yi Sallar Idi A Ranar Asabar – Sheikh Lukuwa

0
249

Daga Usman Nasidi.

WANI malami a jihar Sokoto Sheikh Musa Lukuwa ya bayyana dalilin da ya sa ya jagoranci wasu mutane suka gudanar da sallar Idi a ranar Asabar duk da cewa Sarkin Musulmi ya ce ranar Lahadi za a yi sallar Idi.

A cewar Sultan, ba a ga jaririn watar Shawwal ba a Najeriya wadda hakan na nufin za a gudanar da azumin Ramadan 30.

A hirar wayar tarho da ya yi da Majiyarmu, Lukuwa ya ce, “Sarkin Musulmi ya ce ba a ga wata ba amma mun ga watan saboda haka matsayarmu ta fi ta sarkin.”

A cewarsa, an ga jaririn watan a wurare da dama a Sokoto da wasu garuruwan da ke makwabtaka da jihar kuma an sanar da kwamitin sarkin musulmi amma ba su dauki mataki a kai ba.

Ya kara da cewa an samu sahihan rahoto da ke nuna cewa an ga jaririn watan a Yauri da Kamba a jihar Kebbi da kuma Zariya a jihar Kaduna har ma da Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da mu sun yi Sallar Idi a ranar Asabar.

“Wata dai daya ce kuma idan an gani a wuri daya ya isan ma dukkan musulmin duniya domin Manzon Allah SAW ya umurci musulmi su ajiye azumi idan an ga jaririn wata,” in ji shi.

Lukuwa ya tuna lokacin da marigayi sarkin musulmi ya taba sanar da ganin wata misalin karfe 12 na rana, inda ya kara da cewa marigayi Sultan Ibrahim Dasuki da Muhammmadu Maccido ba su taba kin karbar ganin wata ba don karfe 7 na yamma ta wuce ko kuma don ya saba wa hasashen masana.

Da aka tuntube shi, Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin bayar da shawara a kan harkokin addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaidu sun yi biyaya ga dokar Sarkin Musulmi don shi ne zai iya fadar ranar da za ayi Idi.

Ya kara da cewa ya dauki wannan matakin ne a lokacin da ya samu sanarwar sarkin musulmin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here