El–Rufai Ya Sake Komawa Iyaka Ya Kafa Ya Tsare Don Hana Kanawa Shiga Kaduna

0
232

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

A jiya, Asabar 23 ga watan Mayu, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya sake jagoranci tawagar jami’an gwamnatinsa domin tabbatar da dokar hana shige da fice a tsakanin jihohi.

A ranar Juma’a, Gwamnan tare da tawagarsa sun fita irin wannan aikin domin tabbatar da cewa babu wani matafiyi da ya ketare iyakar jihar ya shigo ba tare da kwakkwaran dalili na aiki ko doka ba.

Mutane da dama kan yi balaguro daga birane daban-daban a jajibirin sallah domin zuwa gida yin bikin sallah tare da iyalansu da sauran ‘yan uwa da abokan arziki.

A kwanan baya dai wani bidiyo ya rika yawo a dandalin sada zumunta inda Gwamnan ke kokawa kan yadda almajiran Kaduna da aka dawo da su daga Kano mafi yawancinsu ke dauke da cutar korona.

Gwamnan ya nuna cewa an saka dokar hana fice da shige tsakanin jihohin ne domin kiyayye lafiyar al’umma amma wasu hukumomin tsaro na karbar kudi suna barin mutane na shiga Kaduna.

Hakan ya sa Gwamnan ya dauki alwashin cewa zai tafi iyakar jiharsa da Kano da kansa ya tabbatar ana biyayya ga dokar ta hana shige da fice musamman a wannan lokaci da sallah.

Gwamnan Kadunan ya wallafa hotuna a shafin gwamnatin jihar na Twitter @GovKaduna

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here