Kungiyar Izala Ta Tallafa Wa Iyalan Shugabannin Kungiyar Da Kayayyakin Abinci A Jos

1
646
Isah Ahmed Daga Jos
KUNGIYAR Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta Kasa, karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta tallafa wa iyalan shugabannin kungiyar da suka rasu, wadanda suke zaune a garin Jos, babban birnin jihar Filato da kayayyakin kayayyakin abinci.
Kayayyakin abincin da kungiyar ta tallafabwa iyalan shugabannin da suka rasun, sun hada  da shinkafa da suga da madara.
Da yake zantawa da wakilinmu bayan kammala mika kayayyakin ga iyalan, shugaban kungiyar na karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jihar ta Filato Alhaji Ya’u Musa Maigado, ya bayyana cewa  gidajen iyalan da suka kai wannan tallafin kayayyakin abinci  sun kai guda 10.
Ya ce gidajen sun hada  da gidan marigayi sheikh Isma’ila Idris da gidan marigayi Sheikh Ibrahim Bawa Maishinkafa da gidan marigayi Sheikh Sa’idu Alhasan Jos da gidan marigayi Sheikh Adamu Ibrahim Mai shafi da dai sauransu.
Ya ce shugaban  kungiya na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya kirkiro wannan shiri, na tallafa wa iyalan tsofaffin shugabannin kungiya da suka rasu, na bangarorin malamai da shugabanni da ‘yan agaji a duk fadin Najeriya.
‘’Gaskiya wannan abu da uwar kungiyar Izala ta yi, wani babban abin koyi ne ga kungiyoyi  da sauran zamantakewa irin ta mutane, na ya kamata  idan ana tare da  mutum, bayan ya rasu kada a manta da iyalansa’’.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here