Sallar Bana Babu Ciniki Sakamakon Annobar Korona-Buhari Zakari

  0
  369
  Isah Ahmed Daga Jos
  WANI dan kasauwa da yake sayar da takalma a kasuwar Takalma ta bayan banki da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato Alhaji Buhari Zakari Wazirin Kafe, ya bayyana cewa sallar bana babu ciniki, sakamakon halin da ake ciki  na annobar korona. Alhaji Buhari Zakari ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
  Ya ce bana jama’a suna zaune ne a gida, basa fita yin sana’o’i kuma  da yawansu ba su da abincin da za su ci, balle su yi tunanin saya wa ‘ya’yansu kayan sallah. Sakamakon wannan annoba, don haka sallar bana, ba a yi cinikin takalma ba.
   Ya ce a shekarun baya, idan irin wannan lokaci ya zo za ka ga iyaye suna turereniya, wajen saya wa ‘ya’yansu da matansu da iyayensu takalma, amma a bana abin ba haka yake ba.
  ‘’Ita shekarar bana kan abin da ya shafi harkokin kasuwanci, ba a  sanya shi a cikin lissafi. Saboda wannan annoba ta korona. Domin gabaki daya a nan Jos, ana fita ne kwanaki uku a mako. Sai dai yadda abu ya zo, haka za a yi hakuri a ci gaba da addu’a, Allah ya kawo mana karshen wannan annoba’’.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here