An Kara Dokar Hana Fita A Kaduna Da Sati Biyu

0
389
Mustapha Imrana Abdullahi
MATAIMAKIYAR Gwamnan Jihar Kaduna Dakta Hadiza Balarabe, ta bayyana wa al’ummar jihar cewa ta kara sanya dokar hana fita da sati biyu.
A cikin sanarwar da ta fitar ta yi godiya ga al’ummar jihar Kaduna bisa irin yadda suka yi biyayya a kwanaki 60 wato tsawon watanni 2 da aka rika sanya dokar na kwanaki 30 da biyu.
Kuma sanarwar ta bayyana cewa za a rika fita a halin yanzu na kwanaki 2 a makon farko na dokar, sannan a fita wasu kwanaki uku wato ranakun Talata, Laraba da Alhamis, wato an samu karin kwana daya kenan sabanin da da ake yin kwanaki 2 a sati.
Idan aka duba dai za a ga a cikin sati biyun za a yi kwanaki 7 kenan cikin dokar hana fita sauran ranakun kuma za a rika samun walwala.
Wannan sanarwar dai ta biyo bayan karewar kwanaki 30 da gwamnatin jihar ta bayyana na dokar a baya.
Sanarwar kuma ta ci gaba da fadakar da jama’a bukatar da ke akwai na yin biyayya ga dokar dakile cutar Covid – 19 da ake kira da Korona bairos.
Da suka hada da a rika wanke hannu, yin amfani da Takunkumin rufe baki da hanci da kuma bayar da tazara tsakanin jama’a tare da kiyaye duk wani taron jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here