Filin Jirgin Saman Yobe Zai Fara Aiki Ba Da Jimawa Kwarai Ba- Mai Mala Buni

0
580
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

GWAMNA Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya bayyana cewar, sabon filin jiragen dakon kaya na kasa da kasa da ke Damaturu zai fara aiki ranar Juma’a 29 ga watan Mayun da muke ciki na 2020.
Cikin bayaninsa yayin ziyarar gani da ido shi da babban kwamandan mayakan saman kasar nan Air Marshal Sadik Abubakar a sabon filin jirgin saman kasa da kasa da ke jihar Gwamna Mai Mala ya ce filin jiragen dakon kayan zai fara ne da gwajin saukar jirage da ake amfani da su na yau da kullum.
Gwamnan ya kara da cewar, gwamantinsa za ta gina barikin sojin sama tare da samar da wadatattun kayayyakin aiki a filin jirgin domin tabbatar da aiki yadda ya kamata don zuwa daidai da zamani.
Gwamnan ya kuma yaba da goyon bayan da gwamnatin tarayya da sojoji da al’umnar jihar suke bayarwa a yaki da ta’addanci a jihar da ake famar yi babu kakkautawa.
Da yake jawabi babban kwamandan mayakan saman Air Marshal Sadiq Abubakar yabawa ya yi bisa yadda Gwamnan ke kokarin samar wa rundunarsa da kyakkyawan yanayin aiki da ya dace da su.
Air Marshal Sadik Abubakar ya kara da cewa, “na ji dadi da Gwamna ya ba mu wurin girke kayan aiki da sojojinmu da ke yaki a jihar ta Yobe wadda haka na matukar karfafa mana gwiwa matuka”.
Ya kara da cewar, “na tabbata hakan zai sa mu yi saurin tunkarar duk wata matsalar tsaro daga cikin jihar Yobe, sabanin daga Maiduguri da muke fama sosai.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here