Gwamna Mai Mala Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Kammala Ibadar Azumi

0
348
Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
GWAMNNA Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya taya al’ummar musulmi murna bisa ga dacewa na kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kiran al’ummar jihar da su dukufa da  addu’ar Allah SWT  ya ci gaba da samar da zaman lafiya a Jihar Yobe da ma kasa baki daya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a sakonsa na Sallah da ya gabatar ga al’ummar Jihar a kafofin yada labarai.
Ya kara da cewar “duk da cewar, watan Ramadan ya wuce, to amma duk da haka akwai bukatar da a yi amfani da darussan da aka samu daga wannan wata musamman ta wajen tausayawa da nuna kauna gami da zaman lafiya da wannan wata ya koyar”.
” A matsayinmu na musulmi muna da kwararan dalilan da zamu godewa Allah SWT dangane da cikakkar lafiyar da ya bamu har muka kai ga samun damar kammala Azumin na watan Ramadan lafiya.”
A Cesar gwamnan kwanannan ne muka fuskanci babban kalubale na cututtuka da ya haddasa rasuwar rayukan ‘yan uwa wadda muke fatan Allah SWT ya jikansu da rahama ya sa Aljanna fiddausi nw makomarsu.
Daga nan sai gwamna Buni ya yabawa al’ummar Jihar Yobe dangane da had in kan da suke bayarwa ga manufofin gwamnatinsu, ” don haka ne zan yi amfani da wannan dama don yabawa da godewa dukkannin al’ummar Jihar don zanan lafiya tsakaninsu da gwamnatinsu Jihar.
“Ya kara da Cesar, addu’o’in da Ku al’ummar ke yi ga gwamnatin ne ya sa muke cimma manufofin mu cikin nasara”.
Gwamnan ya kirayi al’ummar da su ci gaba da addu’ar Allah SWT ya kawar mana annobar dake ddabar kasar nan da ma kasa baki data.
Don haka gwamnan ya bada tabbaci ga al’ummar Jihar Cewar,  gwamnatinsa za ta ci gaba da bada cikakken tsaro ga rayukansu da dukiyoyinsu, kuma zasu ci gaba da kokarin habaka tattalin arzikin Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here