An Cafke ‘Yan Fashi 2 Masu Kwacen Keke-Napep A Anambra

0
422

Daga Usman Nasidi.

RUNDUNAR ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Anambra, ta samu nasarar cafke wasu miyagun mutane biyu da ake zargin su da aikata laifin fashi da makami.

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, wani matukin keke napep, Joseph Asogwa, a ranar Talata ya fada tarkon ‘yan fashi da makami a kan hanyar Onitsha zuwa Owerri a da ke yankin Oba na jihar Anambra.

Miyagun biyu bayan kwatar abin neman abincin na Joseph, sun kuma kwarara masa wani tafasasshen ruwa mai radadin gaske, wanda ya makantar da shi na wani dan lokaci.

Cikin wannan yanayi na karaji da kururuwa ta neman a kawo masa dauki, ya sanya nan da nan jami’an tsaro masu sintiri a hanyar suka cimma masu ta’addar biyu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar wannan mummunan lamari. Ya ce an an cafke ababen zargin biyu tare da baburin mai kafa uku.

Ya ce: “Da misalin karfe 7.55 na ranar 26 ga watan Mayun 2020, a yankin Umuogali da ke kan hanyar Onitsha zuwa Owerri, wasu ‘yan ta’adda biyu da suka yi kaurin suna wajen kwacen keke napep, sun shiga hannu.”

An garkame ‘yan ta’addan da suka shahara da satar keke a ofishin ‘yan sanda na Oba da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here