Daga Yanzu Mun Haramta Almajiranci A Kano – Ganduje

0
390

Daga Usman Nasidi.

GWAMNATIN jihar Kano ta haramta Almajiranci a jiharta kuma ta lashi takobin cewa duk mahaifin da ya tura dansa Almajirci zai gurfana gaban kotu.

Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya alanta hakan ne ranar Laraba yayin da yake hira da manema labarai a gidan gwamnatin jihar.

Amma dai, Gwamnan ya gindaya sharruda da ya wajaba a cika ga duk wanda ke son tara yara don karatun Allo.

Ganduje ya jaddada cewa wajibi ne manhajin karatun ya hada da ilimin Boko kuma wajibi ne malami ya tanadi azuzuwa, wuraren kwana, da isasshen abinci saboda kada yaran su fita bara.

Ya ce: “Gwamnatin jihar ba za ta lamunci Almajiranci a jihar ba. Wajibi ne yara su kasance a makaranta.”

“Wajibi ne makarantar ta bi ka’idojin makaratun Boko ; wajibi ne a samu kwararrun malamai, a rika rubuta jarabawa, da kuma bibiya.”

“Muna tabbatarwa al’ummar jihar cewa ana karantar da ilimin addini a makarantunmu na Boko kuma muna daukar kwararrun Malamai.”

Ya kara da cewa kada hankalin Malaman makarantun Allo ya tashi saboda ba wai ana kokarin kwace musu aiki ba ne, gwamnatin jihar na shirye da daukarsu aiki sashen ilimin jihar.

A bangare guda, shugaban shirin Almajiranci a jihar, Alhaji Sule Garo, ya ce kawo yanzu gwamnatin jihar ta fitar da Almajirai 1,172 zuwa jihohinsu na asali.

Ya ce an tura 419 jihar Katsina, 584 jihar Jigawa, 155 jihar Kaduna, 38 jihar Bauchi, sannan 36 jihar Gombe.

Garo ya kara da cewa jihar ta karbi bakuncin Almajirai kimanin 1000 daga sassan Arewa daban-daban. Akwai 179 daga jihar Adamawa, 220 daga jihar Nasarawa, 96 daga jihar Gombe, 18 daga Katsina, da 82 daga jihar Kaduna, kuma an killacesu na tsawon makonni biyu.

Ya ce kawo yanzu, 733 cikin wadanda aka killace tuni an mayar da su wajen iyayensu.

“Jami’an kiwon lafiyanmu sun gwada dukkan Almajiran kuma yawancinsu ba su da cutar. Wadanda ke dauke da cutar an tafi da su cibiyar killacewa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here